De Mistura ya bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai jim kadan bayan kammala tattaunawa da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov dana tsaro Sergei Shoigu.
Ya ce sabon zagayen tattaunawar ta Geneva zata mayar da hankali ne game da yadda za'a samu cikakken tsarin aiwatar da kudurin kwamitin tsaron MDD mai lamba 2254 wanda aka amince da shi a watan Disambar 2015, wanda ya ayyana bukatar tsara kundin tsarin mulkin kasar da kuma shirya zabe a Syriar.
Wakilin na MDD ya ce, yana sa ran za'a samu taimako daga dukkan bangarorin da abin ya shafa, ciki har da kasar Rasha, domin tabbatar da ganin taron tattaunawar dake tafe ya samu gagarumar nasara sama da wadanda aka shirya a baya, musamman ma wanda aka kammala a farkon wannan watan ba tare da cimma nasara ta azo a gani ba.(Ahmad Fagam)