in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta fara kafa zaunanniyar rundunar sojoji a sansanin sojinta dake Syria
2017-12-27 11:09:17 cri

Ministan harkokin tsaron kasar Rasha Sergey Shoygu ya bayyana a jiya Talata cewa, a halin yanzu, kasar Rasha ta shirya kafa zaunanniyar rundunar sojoji a sansanonin sojanta na Hmeymim da na Tartus.

Bisa labarin da aka samu daga shafin yanar gizo na ma'aikatar harkokin tsaron kasa ta Rasha, an ce, a yayin taron da rundunar sojan kasar ta kira a wannan rana, Sergey Shoygu ya bayyana cewa, shugaban kasar ya sanya hannu kan daftarin da aka gabatar, game da tsarin kafa rundunar sojoji a sansanonin biyu. Sa'an nan, ma'aikatar harkokin tsaron kasar ta fara aiwatar da ayyukan dake da nasaba da hakan.

A ranar 11 ga wata, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da fara janye sojojin kasar daga kasar Syria, ko da yake za a ci gaba da rike sansanin sojojin sama na Hmeymim, da kuma sansanin sojojin teku na Tartus na kasar Rasha dake kasar Syria. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China