in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya sabunta umarnin kai kayayyakin agaji Syria ta kan iyaka
2017-12-20 10:35:42 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya amince da kudurin sabunta umarnin tsallake iyaka domin kai agajin jin kai kasar Syria har na tsawon watannin 12 wato har zuwa ranar 10 ga watan Janairun shekarar 2019.

Kudurin na bukatar hukumomin Syria su gaggauta mayar da martani ga bukatun kai kayayyakin agajin ta kan iyaka da MDD da sauran abokan huldarta za su mika, tare da ba a bukatun muhimmanci

Har ila yau, kudurin yana bukatar sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya gudanar da rubutaccen nazari kan ayyukan ba da agaji ta kan iyaka na MDD, watanni 6 bayan amincewa da kudurin, ciki har da shawarwari kan yadda za a kara karfafa aikin sa ido na majalisar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China