in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin kasashen yammacin duniya ba za su janye daga kasar Syria cikin gajeren lokaci ba
2017-12-30 13:40:30 cri
Mataimakin hafsan sojojin kasashen yammacin duniya dake yaki da kungiyar IS, kuma manjo janar na sojojin Birtaniya Felix Gedney, ya ce sojojin kasashen yammacin duniya ba za su janye daga kasar Syria cikin gajeren lokaci ba.

Felix Gedney ya bayyana yayin wani taron manema labaru da aka yi ta wayar tarho a ma'aikatar harkokin tsaron Amurka cewa, a halin yanzu, mayakan kungiyar IS na da karfin kai hari ga sojojin kasashen yammacin duniya dake karkashin jagorancin Amurka, da kuma ikon kwace yankunan daga hannun gwamnatin kasar Syria. A don haka, Sojojin kasashen yammacin duniya ba za su janye daga kasar Syria ba sai kungiyar IS ta daina zama barazana ga kasar.

Gedney ya bayyana cewa, sojojin kasashen yammacin duniya suna son kama shugaban kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi, amma a yanzu babu wani shiri na kama shi, kana sojojin ba za su mayar da hankali ga wannan aikin ba a yanzu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China