in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Faransa ya ce wajibi ne a yi aiki tare da Assad don gina zaman lafiyar Syria
2017-12-18 11:02:08 cri

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya ce ya yi amana wajibi ne ya tattauna tare da shugaban kasar Syria Bashar al-Assad da wakilansa domin kawo karshen yakin basasar kasar, da kuma shirya hanyoyin da za su tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na France2 na kasar, shugaba Macron ya ce, ya canza matsayarsa game da abin da ya faru a baya, a baya sun yanke shawarar ba za su sake tattaunawa da al-Assad ba. Ya ce za su yi nasara a yakin da suke yi da kungiyar IS a Syria nan da karshen watan Fabrairun shekara mai zuwa.

Da yake bayani game da manufofin gwamnatin Faransa da ta shude, wadda ta tsara cewa dole al-Assad ya sauka daga mulki ba tare da gindaya wasu sharruda ba, Macron ya ce, a yanzu wajibi ne a tattauna da Bashar duk da kasancewar zai amsa tambayoyi game da laifukan da ya aikata.

Tashin hankalin na Syria ya fara ne da zanga-zanga a shekarar 2011, ya yi sanadiyyar mutuwar dubban daruruwan al'ummar kasar, kana ya tilastawa wasu miliyoyin 'yan kasar yin gudun hijira, lamarin da ya jefa yankin turai cikin mummunar matsalar kwararar 'yan gudun hijira.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China