Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce, a daren ranar 5 ga wata, sojojinta dake kasar Siriya sun gano wasu kananan jiragen sama guda 13 wadanda suka kusanci sansanonin sojan Rasha, ciki har da guda 10 wadanda suka nufi sansanin Hmeymim, da wasu guda uku da suka nufi sansanin Tartus. Wadannan jiragen sama marasa matuka sun tashi daga wani guri mai tazarar kilomita hamsin daga sansanonin sojan Rasha. A karshe, sojojin Rasha sun kakkabo guda bakwai daga cikinsu, tare da shawo kan sauran wasu shida, ciki har da guda uku wadanda aka tilasta su sauka a yankin dake hannun sojan Rasha, sauran ukun kuma suka tarwatse lokacin da suke saukowa kasa.
Har wa yau, ma'aikatar tsaron Rasha ta ce, sojojin kasar na binciken ta wace hanya ce mayakan Siriya suka iya samun wadannan kayan yaki na fasahohin zamani. Haka kuma, sojojin Rasha na nazarin nau'o'in abubuwan fashewa dake cikin jiragen saman.(Murtala Zhang)