Liu ya yi wannan kiran yayin taron bainar jama'a da kwamitin sulhu na MDD ya kira kan hana yaduwar makaman kare dangi a tsakanin bangarori wadanda ba su karkashin mallakar gwamnatocin kasashen duniya.
Dangane da wannan batu, Liu Jieyi ya gabatar da shawarwari guda hudu kan yadda za a magance wannan matsala. Na farko, a aiwatar da ra'ayi daya da aka cimma, domin warware matsalar daga tushe. Sa'an nan, ya kamata a karfafa ayyukan kasa da kasa wajen hana yaduwar makaman kare dangi. Haka kuma, a zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa domin kyautata ayyukan da abin ya shafa. A karshe a dauki matakan da suka wajaba, domin aiwatar da kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 1540 a dukkan fannoni.
Bugu da kari, ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya domin ba da gudummawa kan yadda za a kyautata tsarin hana yaduwar makaman kare dangi, yin rigakafin yaduwar makamai da kuma kiyaye zaman lafiya a duniya. (Maryam)