Yayin gwajin a jiya Talata, an fara ne da harba wani makami mai linzami na gwaji daga tsibirin Marshall dake yankin tekun Pacific, sa'an nan aka harba na'urar kakkabo shi daga sansanin sojin sama dake Vandenberg a California, mai nisan kilomita 250 daga arewa maso yammacin birnin Los Angeles.
Da yake tabbatar da nasarar gwajin a ranar Litinin, darakta a sashen lura da makamai masu linzami na helkwatar tsaron Amurka Vice Admiral James Syring, ya ce wannan gwaji shi ne mafi nisa da aka taba yi da wannan na'ura.
Gwajin karshe da Amurka ta yi na wannan na'ura a baya, ya gudana ne a watan Yunin shekarar 2014. An kuma tsara gwajin na wannan karo tun cikin shekarar bara, gabanin shirin da kasar Koriya ta arewa ke yi a lokacin, na yin gwajin makamanta masu linzami masu cin dogon zango.
Sai kuma a wannan karo ne Amurka ta yi na ta gwajin, wanda ya biyo bayan gwaji na uku cikin mako guda da Koriya ta arewan ta yi, kuma karo na 9 cikin wannan shekara.