in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira da a inganta hadin gwiwar kasa da kasa a fannin hana yaduwar makaman kare dangi
2017-03-17 10:56:06 cri

Jiya Alhamis, kwamitin sulhu na MDD ya tattauna kan aikin hukumarsa ta hana yaduwar makaman kare dangi, inda zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD Liu Jieyi, ya yi kira ga kasa da kasa da su kau da ra'ayin yakin cacar baki, da yin kokari tare don kyautata aikin gudanarwa a fannin hana yaduwar makaman kare dangi.

A cikin jawabin da ya gabatar, Mr. Liu Jieyi, ya jaddada cewa, hana yaduwar makaman kare dangi da kuma kayayyakin sufurinsu yana da nasaba da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankalin duniya, wanda ya kasance wani kalubale da ke gaban kasashen duniya gaba daya, kana wani muhimmin batu ne wajen gudanar da harkokin duniya.

Yayin da yake ambaci yadda kasar Sin ta sa hannu cikin harkokin duniya, musamman ma a fannin gudanar da aikin da ke da nasaba da hana yaduwar makaman kare dangi, Mr. Liu ya furta cewa, "kafa makomar bil Adam ta bai daya" wata ka'ida ce da kasar Sin ke bi wajen sa hannu cikin aikin gudanar da harkokin duniya. A cewarsa, kasar Sin za ta ci gaba da hadin gwiwa tare da kasa da kasa, a kokarin bayar da gudummawarta ga ayyukan kyautata tsarin hana yaduwar makaman kare dangi na duniya, da inganta aikin gudanarwa a wannan fanni, gami da kiyaye zaman lafiya da tsaro a duk duniya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China