in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya zartas da kudurin hana kungiyoyin 'yan ta'adda mallakar makamai
2017-08-03 15:07:26 cri
Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani taro jiya Laraba, inda aka zartas da wani kuduri dake son ganin an hana kungiyoyin 'yan ta'adda samun makamai, tare da bukatar kasashen duniya su karfafa hadin-gwiwa, domin katse hanyoyin da kungiyoyin 'yan ta'adda suka bi wajen samun makamai, a wani mataki na kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya.

Darektan gudanarwa na ofishin yaki da miyagun kwayoyi da manyan laifuffuka na Majalisar Dinkin Duniya Yury Fedotov, da darektan cibiyar yaki da ta'addanci ta MDD Jehangir Khan, da mukaddashin darektan gudanarwa na kwamitin yaki da ta'addanci na kwamitin sulhun MDD Chen Weixiong, gami da wasu jami'ai ne suka halarci taron.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China