in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira da a ci gaba da kokarin kawar da barazanar da makamai masu guba ke kawowa kwata-kwata
2017-04-29 14:01:44 cri
Babban daraktan hukumar haramta amfani da makamai masu guba Ahmet Ümzücü, ya ce cikin shekaru 20 da cimma yarjejeniyar hana amfani da makamai masu guba da kafuwar hukumar, kasashen duniya sun cimma nasarori da dama wajen kawar da makamai masu guba, sai dai a shekarun baya-bayan nan, an sake bullo da amfani da makaman, kuma zai yiwu masu tsattsauran ra'ayi su yi mafani da makami masu guba wajen kai farmakin ta'addanci.

A jawabin nasa na jiya, Ahmet Umzucu, ya ce kamata ya yi bangarori daban-daban su ci gaba da karfafa hadin kai, don yin rigakafi da magancewa, har ma da kawar da kalubalen da makamai masu guba ke kawowa baki daya.

A ranar 29 ga watan Afrilun shekarar 1997 ne aka cimma yarjejeniyar hana amfani da makamai masu guba, sannan, aka kafa hedkwatar hukumar Haramta amfani da makamai masu guba a birnin Hague na Netherlands. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China