in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren MDD ya yi gargadi game da karuwar barazanar makaman kare dangi
2018-01-19 11:02:36 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi gardain cewa, a duk ranar Allah ta'ala ana kara samun karuwar barazanar makaman kare dangi a duniya.

Guterres wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis yayin taron muhawarar manyan jami'an kwamitin sulhun MDD game da makaman kare dangi, ya ce tun lokacin da aka kawo karshen yakin cacar baka, duniya ta ke kara dari-dari game da makaman nukiliya, karuwar rashin yarda tsakanin Amurka da Rasha game da batun nukiliya, tababar da ake nuna kan batun yarjejniyar nukiliyar Iran, yadda amfani da makamai masu guba a Syria ya ke haifar da kalubale ga kokarin da duniya ke yi na kawar da irin wadannan makamai masu ta'annati.

Jami'in na MDD ya kara da cewa, halin da ake ciki a zirin Koriya ya kasance mafi tayar da hankali da hadari ga zaman lafiya da kalubalen tsaro ga duniya a wannan lokaci. Ya ce ya damu matuka game da karuwar fito-na-fito da sojoji ke yi da illar da hakan za ta haifar ga zaman lafiyar duniya.

Bugu da kari, ya kuma yi maraba da kafar tattaunawa da kasashen Koriyoyin nan biyu suka bude, musamman a fannin soja, matakin da ya ce zai taimaka matuka wajen kawar da duk wata rashin fahimta da kuma rage zaman zullumi a yankin.

Ya kuma yi fatan kasashen Amurka da Rasha za su bullo da matakan da suka dace na rage makaman da suka mallaka. A bangaren Syria kuma, Guterres ya ce idan har aka sake amfani da makamai masu guba a kasar, to akwai bukatar kasashen duniya su fito da managartan matakai na gano wadanda ke da hannu don ganin an hukuntasu. Ya ce ta haka ne kadai za a kawar da amfani da irin wadannan makamai ba bisa ka'ida ba.

Daga karshe ya bayyana fatan kwamitin sulhun MDD zai hada kai don cimma burin kawar da makaman kare dangi a doron kasa, inda ya ba da misali da hawa kujerar naki da kasar Rasha ta yi game da fadada ikon binciken hadin gwiwa da kungiyar hana yaduwar makamai masu guba da MDD suke yi game da zargin amfani da makamai masu guba a kasar Syria, lamarin da ya kai ga kawo baraka a kungiyar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China