Rahotanni daga ma'aikatun tsaro da na kiwon lafiyar kasar Libya, sun bayyana cewa, a jiya Litinin, wasu mahara sun kai hari a wani wurin dake kusa da filin jirgin sama na MITI Jia a Tripoli, babban birnin kasar. Ya zuwa yanzu, harin ya haddasa rasuwar mutane guda 89, baya ga jiragen sama guda biyar da suka sauka a filin jirgin sama suka lalata.
A wannan rana kuma, gwamnatin hadin kan kasar Libya ta yi Allah wadai da wannan harin. (Maryam)