in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bayyana zabe a matsayin ginshikin tabbatar da zaman lafiya a Libya
2018-01-11 09:28:20 cri

Mataimakin sakatare janar na MDD mai kula da al'amuran siyasa Jeffrey Feltman ya bayyana cewa, aiwatar da zabe shi ne kadai mafitar da za ta tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar Libya.

Feltman ya bayyana hakan ne a taron manema labarai bayan wata ganawa da ta gudana tsakaninsa da firaministan Libyan mai samun goyon bayan MDD Fayez Serraj a Tripoli, babban birnin kasar, inda jami'an biyu suka tattauna game da ci gaban siyasa na baya-bayan nan da aka samu a kasar, da kuma cimma matsaya game da muhimmancin samar da dokar zabe da samar da dokar kundin tsarin mulki kasar wadda za ta ba da damar shirya kuri'ar raba gardama.

Feltman ya ce, babban sakataren MDDr Antonio Guterres, ya kuduri aniyar goyon bayan al'ummar kasar ta Libya wajen shirya kuri'ar raba gardama game da kundin tsarin mulkin kasar, da shirya zabuka da suka hada zabukan yankunan kananan hukumomi da shirya tattaunawar sulhu ta kasar.

Ya ce, a ko da yaushe suna ba da kwarin gwiwa wajen shirya zabe. Alamu sun nuna cewa bangarorin kasar Libyan da shugabannin kasar suna da muradin shirya zabe a kasar, a matsayin babbar dama wadda za ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar.

Jami'in ya ce, MDD a shirye take ta baiwa Libyan dukkan taimako da goyon bayan da za su tabbatar wa kasar komawa tsarin dimokuradiyya nan da shekara mai zuwa.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China