in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun tsaron Libya sun yi nasarar lalata ababen fashewa a Tripoli
2018-01-07 13:52:09 cri
Wasu dakarun tsaron ma'aikatar harkokin cikin gidan Libya, a ranar Asabar sun yi nasarar lalata wasu ababen fashewa a tsakiyar Tripoli babban birnin kasar.

Jami'an wanzar da tsaron sun wallafa a shafinsu na sada zumunta na facebook cewa, bayan wani rahoto da suka samu na wata jaka makare da ababen fashewa wanda aka ajiye a yankin Al-Drebi, a yankin da aka girke jami'an dake aikin sintiri da daddare, an gaggauta sanar da hukumar dake yaki da ayyukan ta'addanci inda jami'anta suka nufi wajen tare da jami'an aikin sintirin.

Hukumar ta kara da cewa jami'an sun killace yankin don tabbatar da tsaron lafiyar fararen hula.

A cewar hukumar wani kwararren jami'in hukumar yaki da ayyukan ta'addanci ne yayi nasarar lalata ababen fashewar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China