in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ceci 'yan gudun hijira 297 a yammacin tekun Libya
2018-01-08 10:35:14 cri
Bisa labarin da aka samu a jiya Lahadi, an ce, sojojin ruwan kasar Libya sun ceto 'yan ci rani ba bisa ka'ida ba 297 a yankin teku dake yammacin kasar Libya, inda suka kuma gano gawawwaki guda biyu.

Kakakin rundunar sojan ruwan Libya Ayob Qassem ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wata tawagar sojoji dake gudanar da aikin sintiri a yankin tekun dake da nisan kilomita 10 da birnin Garrabulli dake yammacin kasar Libya ne suka gano wadannan 'yan gudun hijira, kuma a lokacin da sojojin suka gano su, suna zaune ne a jiragen ruwa irin na roba guda biyu.

Birnin Garrabulli yana da nisan kilomita 50 daga gabashin babban birnin kasar Libya Tripoli, wanda ya kasance muhimmin wuri da 'yan gudun hijira su kan yada zango kafin tashi zuwa kasashen ketare ba bisa ka'ida ba.

Haka kuma, tun daga shekarar 2011, ana ci gaba da samun tabarbarewar yanayin tsaro a kasar Libya, gwamnatin kasar ta kasa daukar sahihan matakai na kare sassan yankin iyakar tekun ta.

Dubban 'yan gudun hijira ne dai ke tashi daga kasar zuwa kasashen Turai ta barauniyar hanya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China