in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a fara aikin kwashe dandazon 'yan Najeriya da suka makale a Libya
2018-01-05 09:32:13 cri
Mahunkun Najeriya sun fara wani gagarumin aiki na kwashe dandazon 'yan kasar da suka makale a kasar Libya.

Kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta a kasar NEMA Sani Datti ne ya shaidawa manema labarai hakan, yana mai cewa tuni tawagar gwamnatin Najeriyar karkashin jagorancin ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Geoffrey Onyema ta isa Libya, domin kaddamar da wannan aiki.

Datti ya kara da cewa, tawagar ta isa birnin Tripoli a ranar Laraba, gabanin fara aiwatar da debe 'yan kasar zuwa gida, aikin da ake fatan farawa a Juma'ar nan.

Jumillar 'yan Najeriya 5,037 ne suke makale a Libya, kuma tuni ofishin diflomasiyyar Najeriyar ya tsara tantance su da tallafin hukumar kasa da kasa mai lura da harkokin shige da fice.

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ne dai ya ba da umarnin kwashe 'yan Najeriyar daga Libya da ma sauran wasu kasashen Afirka zuwa yankunan su na asali. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China