in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe sama da sojoji dubu 5 a yaki da 'yan ta'adda a Benghazin Libya
2018-01-04 10:24:27 cri
Rahotanni daga kasar Libya na cewa, sojojin kasar sama da dubu biyar ne aka kashe a yakin da kasar ke yi da ayyukan ta'addanci a birnin Benghazi dake gabashin kasar.

Mai magana da yawun sojojin kasar ta Libya Ahmad Mismari wanda ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai, ya kuma ce an yi nasarar kawo karshen ayyukan ta'addanci bayan da sojojin kasar suka fatattaki 'yan ta'adda daga sansanin sojan sama dake Benina da kuma Sidi Ekhrebish a gabashin Benghazi.

Mismari ya ce, gwamnati ta yaba da rawar da sojojin kasar suka taka a wannan fafatawa, lamarin da ya kai ga kisan sojoji 5,000 da suka yi shahada, baya ga wasu dubbai da suka rasa wasu sassan jikkinsu sanadiyyar yaki da 'yan ta'dadda a birnin na Benghazi.

Benghazi dai shi ne birni na biyu mafi girma a kasar Libya kana tushen boren shekarar 2011 wanda ya kai ga hambarar da tsohon shugaban kasar marigayi Muammar Gaddafi. Birnin ya kuma shafe shekaru uku yana fama da yaki tsakanin sojojin da janar Khalifa Hafatar ke jagoranta da kuma 'yan tawaye masu tsattsauran ra'ayi.

A ranar Alhamis ne dai sojoji suka sanar da kwace iko da baki dayan yankin Sidi Ekhrebish dake tsakiyar Benghazi, tungar 'yan ta'addan ta karshe a birnin, bayan da aka kwashe sama da watanni biyar ana bata kashi. 'Yan tawaye da dama ne dai suka ranta cikin na kare bayan da sojojin suka kwace iko da yankin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China