in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya kadai ba zata iya magance matsalar bakin haure ba
2018-01-04 10:41:41 cri
Firaiministan Libya dake samun goyon bayan MDD Fayez Serraj, ya bayyana cewa, kasar Libya kadai ba zata iya magance matsalar kwararar bakin haure ba.

Serraj, ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a lokacin ganawa da minista mai kula da harkokin 'yan Kongo dake kasashen waje Emmanuel Ilunga.

A cewar ofishin yada labaran firaiministan, tattaunawar da suka gudanar ta shafi batun karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ne, da kuma hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu wajen yaki da bakin haure ta barauniyar hanya.

A lokacin ganawar, Serraj ya fadawa Ilunga cewa, abu mafi dacewa ga bakin haure shi ne, su zauna a cikin kasashensu na asali don su bada gudunmowa wajen yadda za'a gina cigaban kasashen nasu, ko kuma su bi hanyoyin mafi dacewa na yin bulaguro don kaucewa jefa kansu cikin garari a yayin tafiya ta barauniyar hanya. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China