in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Sin da Bangladesh sun yi atisayen soja a Sudan ta Kudu
2018-01-16 11:04:00 cri
A jiya ne rukuni na 8 na rundunar sojojin injiniya dake aikin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura kasar Sudan ta Kudu da rundunar sojojn kiyaye zaman lafiya ta kasar Bangladesh suka yi atisayen hadin gwiwa a kasar Sudan ta Kudu, domin kyautata kwarewar sojojin kasashen biyu wajen fuskantar ayyukan gaggawa.

A karshen watan Satumba na shekarar 2017 ne rukunin na 8 na rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura kasar Sudan ta Kudu ya isa kasar Sudan ta Kudu, inda yake gudanar da ayyukan injiniya, domin taimakawa sojojin kiyaye zaman lafiya dake yankin da ake yake-yake na kasar Sudan ta Kudu da dabarun aikin injiniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China