Meles Alem, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Habasha, ya bayyana a lokacin zantawa da manema labarai cewa, ana sa ran bangarorin Sudan ta kudun za su cimma matsaya wajen warware tashin hankalin dake addabar kasar ta hanyar amfani da dandalin na HLRF.
A taron da aka gudanar na majalisar ministocin kasashen gabashin Afrika IGAD karo na 59, an amince za'a mayar da hankali wajen amfani da taron dandalin na HLRF don tabbatar da yarjejeniyar tsakaita bude wuta da kuma samar da jin kai ga al'ummar dake bukatar agaji.
Alem, ya jaddada cewa al'ummar kasa da kasa za su dauki dukkan matakan da suka dace idan wannan tattaunawar ta ci tura don ganin an kawo karshen zaman tankiya a tsakanin bangarorin na Sudan ta kudu.
Firaiministan kasar Habasha kuma shugaba kungiyar IGAD na yanzu, Hailemariam Desalegn, ya bayyana a lokacin bude taron cewa, akwai bukatar bangarorin biyu na Sudan ta kudu da ba sa ga maciji da juna su kawar da banbance banbancen dake tsakaninsu.
A cewarsa, IGAD za ta dauki dukkan matakan da suka dace idan wannan tattaunawa ta faskara.(Ahmad Fagam)