in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dawo da ma'aikatan agaji na MDD 6 da aka ceto lami lafiya
2017-12-21 10:59:02 cri
Jami'in hukumar ba da agajin jin kai ta MDD dake kasar Sudan ta Kudu Alain Noudehou ya fidda wata sanarwa a jiya Laraba cewa, ma'aikatan agaji 6 da suka bata a kasar Sudan ta Kudu sun dawo lami lafiya.

Haka kuma, ya ce, ma'aikatan 6 da suka hada da 'yan kasar Sudan ta Kudu guda 5 da na kasar waje guda 1, dake aiki a wasu hukumomin ba da agaji a kasar, na bulaguro ne a kan hanyar Raja zuwa Wau dake yammacin kasar a lokacin da suka bata.

Sanarwar ta kuma mika godiya matuka ga bangarori daban daban da suka taimaka wajen dawo da ma'aikatan agajin 6 lami lafiya, haka kuma, ana fatan bangarorin kasar Sudan ta Kudu da abin ya shafa za su dukufa wajen kare lafiyar ma'aikatan agajin MDD a lokacin da suke kokarin samar da taimakon jin kai ga al'ummomin kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China