in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a gaggauta dawo da ma'aikatan agaji 6 da suka bata lami lafiya
2017-12-20 10:11:34 cri

Hukumar ba da agajin jin kai ta MDD, ta yi kira da a gaggauta mayar da jami'an ba da agaji 6 da suka bata a kasar Sudan ta Kudu biyo bayan hatsaniyar da ta auku tsakanin dakarun gwamnati da 'yan adawa a kusa da garin Raga, ranar Lahadin da ta gabata.

Jami'in hukumar a Sudan ta Kudu Alain Noudehou, ya yi kira ga bangarori masu fada da juna, su mutunta aikin ba da agajin da ba ya goyon bayan wani bangare a kasar mafi karancin shekaru a duniya.

Wata sanarwar da jami'in hukumar ya fitar, ta ce ma'aikatan 6 da suka hada da 'yan kasar 5 da na kasar waje guda, dake aiki da wasu hukumomin ba da agaji biyu na kasashen waje da kuma guda na kasar, na bulaguro ne a kan titin Raja zuwa Wau a lokacin da suka bata.

Alain Noudehou ya kuma jaddada bukatar dukkan bangarorin su taimaka wajen tabbatar da tsaron jami'an ba da agaji da kuma ba su damar kai dauki ga mutane masu rauni dake fadin kasar.

Rundunar SPLA ta kasar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, 'yan tawaye sun sace wasu mutane 10, bayan sun kai wa motoci biyu hari, ciki har da wata babbar mota dake kan hanyar Raja zuwa Mangayet, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 2. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China