in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya tsawaita aikin shirin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2017-12-15 13:55:36 cri
Daukacin mambobin kwamitin sulhu na MDD ne suka amince da kudurin tsawaita aikin shirin wanzar da zaman lafiya na UNMISS a Sudan ta Kudu da watanni 3, domin kammala nazarin aikin shirin.

Kwamitin ya kuma fitar da wata sanarwa kan kasar, inda ya bayyana dimbin damuwa game da al'amuran da suka shafi siyasa da tsaro da agajin jin kai da hakkokin bil adama da tattalin arziki a kasar da yaki ya daidaita.

Sanarwar ta kuma ruwaito kwamitin na bayyana matsananciyar damuwa game da ayyukan bangarorin dake rikici, wadanda ke kara ta'azzara yanayin da ake ciki, inda a yanzu kasar ke da mutane miliyan 7.6 dake tsananin bukatar agaji da wasu miliyan 4 kuma da suka rasa matsugunansu, yayin da miliyan 6 ke rashin abun da za su ciyar da kansu.

Har ila yau, kwamitin ya ce bangarorin dake rikicin sun gaza girmama kudurinsu na tsagaita bude wuta tare da ba kayakin agaji damar isa ga mabukata ba tare da wata matsala ba.

Sanarwar ta kuma yi kira ga Gwamnatin kasar ta daina bude wuta ta yi biyayya ga shirinta na tsagaita bude wuta, ya na mai kira ga bangarorin adawar su ma su kiyaye.

Kwamitin ya yi kakkausar kira ga bangarorin, su tattauna karkashin tsare-tsaren nahiyar Afrika domin dawo da zaman lafiya kasar. (Fa'iza)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China