in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNHCR ta bukaci a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Sudan ta Kudu
2017-12-24 12:29:34 cri
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta sanar a jiya Asabar cewa, ana farin ciki kan yadda gwamnatin kasar Sudan ta Kudu da 'yan adawar kasar suka daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kwanakin baya, haka kuma hukumar ta yi kira ga bangarorin da ba sa ga maciji da juna a kasar, da su aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.

A cewar sanarwar, wannan yarjejeniyar ta samar da damar saukaka radadin da al'ummar kasar Sudan ta Kudu suke ji sakamakon wutar yaki da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar. Sa'an nan an yi kira ga bangarorin kasar da su yi biyayya ga tanadin dake kunshe cikin yarjejeniyar ka-in da na-in, don biyan bukatun jama'ar kasar na samun kwanciyar hankali da lumana.

Kafin haka, gwamnatin kasar Sudan ta Kudu da 'yan adawa sun sa hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a birnin Addis Ababa na kasar Habasha a ranar Alhamis da ta gabata. Wannan yarjejeniyar ta kayyade cewa, bangarorin da suke yaki da juna za su dakatar da bude wuta, da daina nuna karfin tuwo ta ko wace fuska, da baiwa masu gudanar da aikin jin kai damar shiga yankunan da ake da bukatar agaji. An ce yarjejeniyar za ta fara aiki ne a yau Lahadi, wadda ta kasance wani muhimmin mataki ga yunkurin kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekaru 4 ana gwabzawa a kasar.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China