in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe sansanin tsaron fararen hula na farko a Sudan ta Kudu
2017-12-21 15:11:40 cri
Tawagar musamman ta MDD dake kasar Sudan ta Kudu ta bayar da sanarwa a jiya Laraba cewa, a sakamakon kyautatuwar yanayin tsaro a wasu yankunan kasar Sudan ta Kudu, wasu da suka kauracewa gidajensu sakamakon fargabar tashin hankali sun koma garuruwansu, don haka an rufe sansanin tabbatar da tsaron fararen hula na farko.

Sanarwar ta bayyana cewa, wannan ne sansani na farko na tabbatar da tsaron fararen hula da aka rufe a kasar Sudan ta Kudun, tun bayan barkewar yakin basasar kasar a watan Disambar shekarar 2013. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China