in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar likitoci da Sin ta tura Mozambique ta kammala ayyukanta a kasar cikin nasara
2018-01-15 11:00:34 cri
Yau da safe ne tawagar likitocin sojoji ta farko da kasar Sin ta tura kasar Mozambique ta kama hanyar dawowa kasar Sin bayan kammala ayyukanta na ba da taimako a kasar cikin nasara.

Alkaluman kididdigar da tawagar ta fitar sun nuna cewa, a lokacin da likitoci guda tara suke gudanar da ayyukansu a asitibin sojoji na Maputo, gaba daya sun ba da jinya ga mutane kimanin guda 3000, kana sun yi aikin tiyata sama da 40, inda suka kuma samu yabuwa matuka daga sojojin kasar Mozambique da wadanda suka samu jinya, saboda kokari da kuma kwarewarsu ta ba da jinya.

A yayin bikin ban kwana da aka shirya musu a jiya jakadan kasar Sin dake kasar Mozambique Su Jian ya bayyana cewa, tawagar likitocin da kasar Sin ta turo kasar Mozambique ta nuna aniyar kasashen biyu ta karfafa mu'amalar dake tsakaninsu a fannin likitocin sojoji, da karfafa dangantakar abokantaka dake tsakanin kasar Sin da kasar Mozambique bisa manyan tsare-tsare.

A nasa bangare, shugaban asibitin sojojin Maputo ya bayyana cewa, cikin watanni biyu da suka gabata, likitocin kasar Sin da takwarorinsu na kasar Mozambique sun kulla dangantakar abokantaka mai kyau a tsakaninsu. A sa'i daya kuma, suna fatan kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasarsa a fannin horas da likitocin kasar da samar da na'urorin zamani. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China