Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan Inacio Dina, ya bayanawa taron manema labarai cewa, nau'in muggun laifukan da aka aikata yana daga cikin ayyukan ta'addanci, kuma za'a hukunta wadanda suka aikata laifin gwargwadon girman laifinsu.
A ranar 5 ga watan Oktoban shekarar 2017, wasu gungun masu dauke da makamai su 30 suka kaddamar da hare hare ba tare da kakkautawa ba kan ofisoshin 'yan sanda 3 a Mocimboa da Praia, lamarin da yayi sanadiyyar kashe 'yan sanda 2 da kuma wani shugaban al'umma a rana guda.
Kawo yanzu, 'yan sanda sun cafke mutane 251 wadanda ake zarginsu da hannu wajen aikata laifin. Kana jami'an 'yan sandan sun bayyana cewa, suna samun galaba kan gungun masu laifin, kuma mazauna wadannan yankuna suna zama cikin dar dar, inda suke fargaba game da makomar rayukansu da dukiyoyinsu. (Ahmad)