in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 117 sun mutu a sakamakon ruwan sama da ya sheka kamar da bakin kwarya
2017-02-28 10:54:35 cri
Sashen ba da kariya ga al'umma na kasar Zimbabuwe ya bayana a jiya Litinin, cewa, an sheka ruwan sama fiye da kima a daminar da ta fara daga watan Nuwamban bara, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 117, tare da jikkata wasu 106.

Kawo yanzu, ruwan sama ya rushe gidaje 1930 a kasar, baya ga makarantu 71 da asibitoci 5 da kuma madatsan ruwa 71 da suka lalace. Ruwan sama ya kuma rushe wasu hanyoyin mota da ma gadoji.

Rahotanni na nuni da cewa, goguwa mai lakabin Dineo da ta sauka a kudancin kasar Mozambique a ranar 15 ga watan Faburairun ita ma ta kawo illa ga kasar Zimbabuwe, wadda ta tagayyara mutane sama da dubu a sakamakon yadda ruwan saman da take tafe shi wanda ya lalata gidajensu.

Yanzu haka gwamnatin kasar ta Zimbabuwe da ma kungiyar Red Cross da sauran kungiyoyin duniya suna samar da abinci da ruwan sha da gidajen kwana na wucin gadi da jiyya ga al'ummar da bala'in ya shafa. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China