in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Iran ba ta amince da gyaran da aka yiwa yarjejeniyar nukiliyar kasar ba
2018-01-15 10:11:23 cri
Rahotanni daga kasar Iran na cewa, shugaban majalisar dokokin kasar Iran Ali Larijani ya sanar da cewa, majalisar ba ta amince da gyaran da aka yiwa yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran, wadda aka kulla a watan Yuli na shekarar 2015 ba.

Haka kuma, a yayin zaman mambobin majalisar dokokin kasar da aka yi a babban birnin kasar, Tehran, Mr. Larijani ya bayyana cewa, maganar da shugaban kasar Amurka ya yi game da yarjejeniyar nukiliyar kasar ta Iran za ta lalata yarjejeniyar da kasashen duniya suka kulla.

A ranar 12 ga wata ne, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya tsai da kudurin sake tsawaita takunkumin da aka kakaba wa kasar Iran a kan yarjejeniyar nukiliyar kasar. A sa'i daya kuma, ma'aikatar harkokin kudin kasar Amurka ta sanyawa 'yan kasar Iran 14 da wasu kamfanonin kasar takunkumi, bisa zargin cewa, sun keta hakkin dan Adam, ko kuma sun taimakawa shirin kire makamai masu linzami na kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China