in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin kudi ta Amurka ta sanar da sakawa kamfanoni 5 na Iran takunkumi
2018-01-05 11:45:32 cri
Ma'aikatar harkokin kudi ta kasar Amurka ta sanar a jiya Alhamis cewa, ta sakawa kamfanoni 5 na kasar Iran takunkumi, bisa zargin su da nuna goyon baya ga shirin nazarin makamai masu linzami na kasar.

Ma'aikatar harkokin kudin Amurkan ta gabatar da sanarwa a wannan rana dake cewa, wadannan kamfanoni 5 da aka sakawa takunkumi a wannan karo, suna karkashin mallakar wani gungun masana'antu na kasar ta Iran. Ma'aikatar ta zargi kamfanonin 5 da shiga aikin nazarin makamai masu linzami na kasar Iran, da samar da goyon baya ga aikin a fannin fasahohi da sauransu.

Bisa matakan takunkumin da aka kakaba musu, za a dakatar da yin amfani da kudi ga kamfanonin 5 a kasar Amurka, kana an hana 'yan kasar Amurka su yi musayar ciniki tare da su.

Bayan da Donald Trump ya kama aiki a matsayin shugaban kasar Amurka a watan Janairu na bara, gwamnatin kasar Amurka ta yiwa kasar Iran matsin lamba bisa aikin kasar na raya makamai masu linzami, tare da daukar matakan kakaba mata takunkumi da dama. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China