A jiya Alhamis ne dai jagoran ofishin dake lura da harkokin kasashen waje na kungiyar tarayya Turai EU Federica Mogherini, da ministocin harkokin wajen kasashen Faransa, da Jamus, da Birtaniya, suka gana da takwaran su na kasar Iran Mohammad Javad Zarif, inda suka bayyana masa gamsuwar su game da yadda ake aiwatar da wannan yarjejeniya.
Hakan dai na zuwa ne yayin da ake dakon matakin da shugaban Amurka Donald Trump zai dauka game kakabawa Iran din takunkumi.
A ranar 13 ga watan Oktobar da ya shude ne dai shugaba Trump ya bayyana rashin gamsuwar sa da yadda Iran ke aiwatar da waccan yarjejeniya. To sai dai kuma cikin watanni 2 da suka gabata, majalissar dokokin Amurka ba ta zartas da wani kuduri game da kakabawa Iran din takunkumi ba. Kuma hakan na nufin shugaban Amurkan, na da ikon yanke shawarar daukar matakin kakabawa Iran din sabon takunkumin makamashi, ko kuma ya ayyana wani matakin na daban.(Saminu Alhassan)