Kwanan baya, an yi zanga-zanga a birane da dama a kasar Iran, domin nuna adawa da karuwar farashin kayayyaki a kasar da wasu batutuwan dake shafar wahalar zaman rayuwar al'ummomin kasa ta Iran.
Haka kuma, bisa labarin da aka samu daga kafar watsa labarai mallakar gwamnatin kasar Iran, an ce, zanga-zanga a biranen kasar sun haddasa tashe-tashen hankula a wasu wurare. (Maryam)