in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta kira taron tattaunawa kan yanayin Iran
2018-01-06 13:09:04 cri
A ranar 5 ga wata, bisa bukatun kasar Amurka, kwamitin sulhu na MDD ya kira taron tattaunawa kan yanayin da kasar Iran ke ciki.

Zaunanniyar wakiliya ta kasar Amurka dake MDD Nikki Haley ta yi zargi mai tsanani kan yanayin kasar Iran.

Amma, a nasa bangaren, zaunannen wakilin kasar Iran Gholamali Khoshroo ya yi zargin cewa, kasar Amurka tana matsawa kasar Iran lamba a matsayinta na zaunanniyar mamba ta kwamitin sulhu na MDD, inda ta yi tattaunawa kan harkokin cikin gidan kasar ta Iran a kwamitin sulhu na MDD. Haka kuma, ya ce, kasar Amurka tana yin shisshigi cikin harkokin yankin Gabas ta tsakiya, wannan shi ne babban dalilin da ya haddasa tashe-tashen hankula a wannan yanki.

Mukaddashin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao, ya jaddada cewa, kasar Sin ta sami labarai game da sauye-sauyen yanayi a kasar Iran, kuma tana fatan za a shimfida kwanciyar hankali a duk fadin kasar bisa kokarin da gwamnatin kasar Iran din da kuma dukkanin al'ummominta suka yi cikin hadin gwiwa.

Haka kuma, Mr. Wu ya ce, yanayin kasar Iran bai haifar da matsala ga zaman lafiya da kuma tsaron kasa da kasa ba, kuma harkar ba ta cikin jadawalin tarukan kwamitin sulhu na MDD. Shi ya sa, yin tattaunawa kan yanayin kasar Iran a kwamitin sulhu na MDD ya saba da kundin tsarin MDD, kuma ba zai ba da taimako wajen warware matsalar da gwamnatin kasar Iran take fuskanta a kasarta ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China