in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci a mutunta yarjejeniyar makaman nukiliyar Iran
2018-01-14 13:09:30 cri

A jiya Asabar kasar Sin ta bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su mutunta yarjejeniyar makaman nukiliyar kasar Iran, bayan da Amurka ta yanke shawarar kara wa'adin dagewa Iran din takunkumin tattalin arzikin da aka sanya mata.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, shi ne ya yi wannan tsokaci a lokacin da aka nemi ya yi karin haske game da matakin na Amurka.

Kasar Sin ta lura cewa kasa da kasa sun goyi bayan cikakkiyar yarjejeniyar nan ta Joint Comprehensive Plan of Action wato (JCPOA) a takaice, wadda ta kunshi cikakken tsarin aiwatar da yarjejeniyar shirin dakatar da makaman na Iran, in ji Lu.

Ya ce kasar Sin tana bada cikakken goyon baya ga yarjejeniyar ta JCPOA, ya kara da cewa, wannan yarjejeniya ba wai tana da muhimmanci ga nasarar da gamayyar kasashen duniya suka cimma ba ne, har ma ta kasance abin misali wajen warware duk wasu batutuwa masu muhimmanci na kasa da kasa ta hanyar amfani da matakan siyasa da na diplomasiyya.

Lu ya ce, domin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar, hakan yana da matukar alfanu wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya, kuma zai taimaka wajen dakile yaduwar haramtattun makamai tsakanin kasa da kasa, wanda hakan shi ne burin dukkannin bangarorin duniya.

A halin da ake ciki a yanzu, kasar Sin tana fata dukkan bangarorin da abin ya shafa za su yi amfani da matakai na siyasa, kuma su kawar da duk wani bambance-bambance dake tsakani, kana su cigaba da aiwatar da yarjejeniyar ta ko wace irin fuska.

Mista Lu, ya nanata matsayin kasar Sin cewa, a ko da yaushe ba ta amince da wata kasa ta sanya wa wata daban takunkumi na kashin kai bisa dokokin kasarta kawai ba. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China