in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha da Iran za su mutunta yarjejeniyar nukiliya
2018-01-11 10:00:05 cri

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, da takwaransa na kasar Iran Mohammad Javad Zarif, sun tabbatar da cewa, za su amince da batun yarjejeniyar kasa da kasa kan dakatar da shirin nukiliyar kasar Iran.

A wata sanarwa da aka fitar bayan kammala ganawar ministocin biyu, jami'an sun bayyana cewa, a shirye suke su ci gaba da mutunta yarjejeniyar, karkashin wata cikakkiyar yarjejeniyar hadin gwiwa wato JCPOA.

Sanarwar ta ce, duk wani yunkurin warwaza yarjejeniyar ta JCPOA wanda ake tunanin Amurka za ta iya haddasawa, hakan ya ci karo da yarjejeniyar kasa da kasa da tabbatar da tsaron shiyyoyi kana lamarin zai iya yin illa ga kokarin da kasashe duniya ke yi na kokarin dakile bazuwar makaman nukiliya a duniya.

An cimma yarjejeniyar ta JCPOA ne, tsakanin Iran da kasashe 5 masu wakilci na dindindin a kwamitin tsaron MDD wato kasashen Birtaniya, Sin, Faransa, Rasha, da Amurka, sai kuma Jamus, a watan Yulin shekarar 2015.

Karkashin yarjejeniyar, Iran ta amince za ta dakatar da shirinta na kera makaman nukiliya domin neman kasa da kasa su dage mata takunkumin da aka aza mata da ba ta taimakon tattalin arziki.

Sai dai kuma, a watan Oktoban 2017, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya soki lamirin yarjejeniyar, inda ya zargi Iran da laifin saba ka'idoji masu yawa, zargin da Iran din ta sha musantawa.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China