in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Iran: Jama'ar kasar suna da ikon bayyana bukatunsu
2018-01-02 13:09:29 cri

Tun bayan da zanga-zangar kin amincewa da karuwar farashin kaya da yawan mutanen da suka rasa ayyukan yi a birnin Mashhad na kasar Iran a ranar 28 ga watan Disambar bara, wata sabuwar zanga-zanga ta barke a birane da daman a kasar, ciki har da babban birnin kasar Tehran. A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar Hassan Rouhani ya bayyana game da wannan batu a ranar 31 ga watan Disamba cewa, jama'ar kasar suna da 'yancin bayyana bukatunsu ta hanyar da ta dace, gwamnatin kasar za ta yi kokarin warware matsalolin da 'yan kasar ke fuskanta.

A jawabin da ya yiwa taron majalisar ministocin kasar a ranar 31 ga watan Disamba cewa, shugaba Rouhanni ya ce yanzu kasar ke fama da matsaloli na rashin aiki, bunkasuwar tattalin arziki, da yaki da cin hanci da rashawa, don haka akwai bukatar da warware wadannan matsaloli,

kuma tilas ne gwamnatin kasar Iran ta gudanar da ayyuka bisa sa idon da jama'ar suke yi.

Game da goyon bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya nuna ga zanga-zangar da ta barke a birane da dama a kasar ta Iran, Rouhani ya mayar da martani cewa, wancan mutum dake fadar shugaban kasar Amurka ya nuna goyon baya ga masu zanga-zangar, amma ya manta da matsayinsa na maida kasar Iran a matsayin kasar da ta nuna goyon baya ga ta'addanci. Wannan mutum ba ya goyon bayan kasar Iran, ba shi da 'yanci a kan jama'ar kasar Iran ba.

A halin yanzu, mutane da dama ne suka mutu a sakamakon zanga-zangar, kana an kama mutane da dama. Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa, ya kamata a girmama bukatun jama'ar kasar da suke dace kan farashin kaya da samar da aiki, bai kamata a ba da dama ga kasashen waje don su yi amfani da su wajen cimma burinsu ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China