in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Isra'ila ya musunta labarin sa kaimi ga yin zanga-zanga a Iran
2018-01-02 13:19:48 cri
Firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya musunta labarin da aka bayar cewa, kasar Isra'ila na daya daga cikin bangarori da suka nuna goyon baya ga yin zanga-zanga a kasar Iran.

Netanyahu ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, zargin da ake yiwa kasar Isra'ila na cewa, tana da nasaba da zanga-zangar da aka yi a kasar Iran kuskure ne.

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Isra'ila suka bayar a ranar 1 ga wannan wata, an ce, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya zargi kasar Amurka da Isra'ila da suka sa kaimi ga yin zanga-zanga a kasar Iran a gun wani taro. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China