in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta yi Allah wadai da harin da Saudiyya ta jagoranta kan wata kasuwa a Yemen
2017-12-28 11:25:04 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah wadai da hare hare ta jiragen sama na baya bayan nan da kasar Saudiyya ta jagoranta wanda aka kaddamar kan kasuwar Taiz dake kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyyar hallaka rayuka masu yawa.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ta Iran, Bahram Qasemi, ya bayyana cewa, lamarin abin takaici ne kuma ya kasance hari na ba zata, wanda aka kaddamar da muggan makamai wanda Amurka ta kera su, wanda ya ce kasar Saudiyyan ta yi amfani da su.

Wasu jiragen saman yaki na dakarun da Saudiyya ke jagoranta ne suka kaddamar da hare hare a kasuwar mai cinkoson jama'a dake kudu maso yammacin lardin Taiz a Yemen a ranar Talata, inda mutane sama da 40 suka hallaka.

Dakarun wadanda Saudiyyan ke jagoranta suna kai hare hare ne a matsayin kai dauki da nufin tallafawa shugaban kasar Yemen Abd-Rabbu Mansour Hadi, wajen murkushe 'yan tawayen Houthi mabiya mazahabar Shiite don kawo karshen tashin hankalin kasar, wanda ya barke tun a watan Maris na shekarar 2015.

Sama da mutanen Yemen 10,000 ne suka mutu tun bayan barkewar tashin hankalin, galibinsu kananan yara ne, kana sama da mutanen kasar miliyan 3 ne rikicin ya raba su da matsugunansu, lamarin da ya haifar da tagayyarar bil adama mafi muni a duniya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China