Rahoton yace, daga cikin adadin mutanen 433 da suka mutu har da kanana yara 79 da kuma mata 10.
Baki daya an hallaka mutane kimanin 201 a kisan kiyashin da suka faru a sassan kasar daban daban, musamman wadanda kungiyoyin masu dauke da makamai suka kaddamar.
Bugu da kari, an hallaka fararen hula kimanin 157 a sanadiyyar nakiyoyi da aka binne a karkashin kasa a yankunan Benghazi, Sirte da Derna, inji rahoton.
Hukumar ta tabbatar da cewa an kama mutane 143 inda aka muzguna musu, yayin da aka yi garkuwa da wasu mutanen 186 a cikin shekarar ta 2017.
A cewar rahoton, a kalla akwai mutane miliyan 3.5 dake cikin kuncin rayuwa a kasar ta Libya, yayin da kusan mutane 400,000 suka kauracewa matsugunansu a kasar.
Matsalar rikicin siyasa, da durkushewar tattalin arziki da tashe tashen hankula na daga cikin matsalolin da suka dagula al'amurra a kasar ta Libya.(Ahmad Fagam)