in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambiya na fama da cutar kwalara
2018-01-10 15:35:43 cri

Ministan harkokin kiwon lafiya na kasar Zambia Chitalu Chilufya ya bayyana a wani taron manema labaru jiya Talata cewa, ya zuwa yanzu, mutane 2802 ne suka kamu da cutar kwalara a kasar, yayin da mutane 64 suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da wannan cuta. Yanzu haka dai masu fama da cutar 218 na samun jinya a kasar.

Ministan ya kara da cewa, daga ranar 10 ga wata, ma'aikatar ta fara yi wa mutane miliyan 2 allurar rigakafin cutar a wasu wuraren da aka fi fama da cutar dake birnin Lusaka. Ya ce za a shafe kwanaki 7 zuwa 10 ana gudanar da aikin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China