in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambia na shirin zama kasar dake kan gaba wajen fitar da kifaye
2017-06-06 10:18:19 cri
Rahotanni daga kasar Zambia na nuna cewa, nan da shekaru biyu masu zuwa kasar tana shirin zama kasar dake sahun gaba a nahiyar Afirka wajen fitar da kifi da kayayyakin da suke da nasaba da kifaye zuwa ketare.

Ministan kiwon kifi da dabbobi na kasar Micheal Katambo wanda ya bayyana hakan, ya ce an samu wannan nasara ce sakamkon yadda aka kara zuba jari a bangaren kiwon kifin kasar.

Ministan ya ce, baya ga batun zuba jari da aka zuba a wannan bangare, ana kuma daukar wasu managartan matakai da nufin bunkasa kiwon kifi.

Yanzu haka dai gwamnatin Zambiar ta karbi rancen dala miliyan 50 daga bankin raya Afirka domin kara bunkasa sana'ar kiwon kifi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China