in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zambiya ya gargadi jami'an diplomasiyya su guji yin katsalandan
2017-04-16 12:23:58 cri
Shugaban kasar Zambiya Edger Lungu, ya gargadi ma'aikatan diplomasiyya da su guji tsoma baki cikin harkokin da suka shafi al'amurran cikin gida na kasar.

Kafofin watsa labarai da dama sun yada rahoto game da kalaman da shugaban Zambiyan, inda yake yin gargadi ga jami'an diplomasiyyar bayan da aka kama madugun 'yan adawar kasar Hakainde Hichilema wanda ake zarginsa da laifin cin amanar kasa ta hanyar yunkurin ta da zaune tsaye a kasar wadda ke kudancin Afrika.

Kasar Amurka da tarayyar Turai sun fitar da wata takarda inda suke bayyana damuwa game da barazanar barkewar rikicin siyasa a kasar.

Wata kafar yada labarai ta cikin gida a kasar, ta wallafa a shafinta na intanet inda ta rawaito shugaban na Zambiya yana gargadin jami'an kasa da kasa da kada su yi shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar, kasancewar Zambiya kasa ce mai cin gashin kanta.

Shugaba Lungu ya ce shi kansa, ba zai yi katsalandan cikin wannan al'amari ba, zai kyale doka ne ta yi aikinta. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China