Ministan ma'adanai na kasar Christopher Yaluma, shi ne ya tabbatar da hakan, ya ce gwamnatin kasar za ta kammala aikin mayar da tsarin samar da lasisin a fannin ma'adanai ta hanyar na'urar kwamfuta da kuma shafukan intanet domin ya dace da zamani, kana domin aikin ya dinga gudana cikin sauri.
Ya ce idan shirin ya tabbata, zai kara janyo hankulan masu zuba jari a fannin hakar ma'adinan kasar, kuma zai bada damar gudanar da aikin samar da lasisin ba tare da rufa rufa ba.
Cikin wani jawabi da ministan ya gabatar a gaban majalisar dokokin kasar ya ce "za'a samu karuwar masu zuba jari a fannin ma'adanan, kuma gwamnati za ta samu karin kudaden shiga ta hanyar kudaden da masu yin rajistar neman lasisin za su biya." (Ahmad Fagam)