in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambiya tana kokarin lalubo hanyar magance kalubalen da cigaban birane zai iya haifarwa
2017-06-07 10:11:02 cri

Wani babban jami'in gwamnatin kasar Zambiya yace, gwamnati tana shirin fito da wani sabon shiri wanda zai warware kalubalolin da saurin bunkasuwar biranen kasar zai iya haifarwa

Ministan kananan hukumomin kasar Vincent Mwale ya bayyana cewa, gwamnatin kasar ta fara gyaran fuska ga wasu dokoki domin shawo kan kalubalolin da cigaba biranen kasar za su iya haifarwa.

Da yake jawabi a wajen taron wuni biyu game da tsara shirin cigaban birane, ministan ya ce matakan da ake shirin dauka, za su tabbatar da cigaban kasar da kuma kyautata yanayin zaman rayuwar al'ummar kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China