Shugaban kwamitin Lasheen Ibrahim ya bayyana a yayin taron manema labarai cewa, za a gabatar da sakamakon babban zaben shugaban kasa a ranar 2 ga watan Afrilu. Amma idan akwai bukatar gudanar da jefa kuri'u zagaye na biyu, al'ummar kasar da suke zaune a kasashen ketare za su iya jefa kuri'unsu daga ranar 19 zuwa ranar 21 ga watan Afrilu, yayin da al'ummar kasar za su jefa kuri'unsu daga ranar 24 zuwa ranar 26 ga watan Afrilu, kuma za a gabatar da sakamakon zaben a ranar 1 ga watan Mayu.
Bisa labarin da aka samu, an ce, 'yan takara za su fara yin rajista a hedkwatar kwamitin kula da harkokin zaben kasar tun daga ranar 20 zuwa ranar 29 ga watan nan da muke ciki, kuma za a gabatar da jerin sunayen 'yan takara a ranar 23 ga watan Fabrairu mai zuwa, bayan an gudanar da bincike yadda ya kamata. (Maryam)