in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar na fatan bankin duniya zai shiga tsakani game da batun madatsar ruwan Habasha
2017-12-27 09:44:24 cri
Mahukuntan kasar Masar sun bayyana bukatarsu, ta sanya babban bankin duniya ya zama mai shiga tsakani, game da takaddamar da kasar ke yi da Habasha kan ginin babbar madatsar ruwan Habasha ko GERD a takaice.

Wata sanarwa da kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Masar Ahmed Abu Zeid ya fitar, ta ce kasarsa na bukatar babban bankin duniya ya yanke shawarar karshe cikin adalci, game da tasirin da madatsar ruwan ta GERD za ta yi ga kogin Nilu, wanda kasashen Masar da Sudan da kuma Habasha ke cin gajiyarsa.

Wannan kuduri dai ya biyo bayan tattaunawar birnin Addis Ababa tsakanin ministan harkokin wajen Masar din Sameh Shoukry, da takwaran sa na Habasha Workneh Gebeyehu.

Wakilan kasashen 3 dai sun sha tattaunawa, da nufin kawo karshen sabanin dake tsakaninsu game da ginin wannan madatsar ruwa ba tare da cimma wata nasara ba. Ko da yake Habasha da Sudan na fatan cimma gajiya mai dimbin yawa daga Dam din na GERD, a hannu guda kuma, Masar na ganin madatsar ruwan za ta janye mata nata kaso na albarkatun ruwan da take amfana daga kogin Nilu.

A watan Maris na shekarar 2015 ne dai shugabannin kasar Masar, da na Habasha da Sudan, suka sanya hannu kan yarjejeniyar raba albarkatun ruwan kogin Nilu, da ma batun ginin madatsar ruwan ta GERD, wadda za ta kasance mafi girma a duk fadin nahiyar Afirka.

Sai dai a daya hannun Shoukry ya bukaci Gebeyehu, da ya tabbatar Habasha ta mutunta tanajin yarjejeniyar da suka cimma, ciki har da batun nazari tare da amincewa da sakamakon tasirin Dam din ga kasashen 3, kafin a kai ga fara amfani da shi gadan gadan.

Kakakin ma'akatar harkokin wajen Masar ya ce Habasha ta yi alkawarin nazartar wannan shawara, kuma za ta maida martani kan hakan ba tare da bata lokaci ba, yayin da kuma nan gaba kadan za a mika makamanciyar wannan bukata ga mahukuntan kasar ta Sudan. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China