in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Masar ya ce harin da aka kai wa wata majami'a ba zai raunana niyyar kasar ta yaki da ta'addanci ba
2017-12-30 13:32:50 cri
Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya ce harin ta'addancin da aka kai wa majami'ar Mar Mina ta birnin Alkahira a jiya, ba zai taba raunana kudurin jama'ar kasar na kawar da ta'addanci ba.

Shugaba al-Sisi ya bayyana haka ne cikin wata sanarwar da fadarsa ta fitar a jiya, inda ya yi wa iyalan mutanen da suka mutu sakamakon harin ta'aziyya, tare da jinjinawa jami'an tsaron da suka dakile maharan. Shugaban ya umarci hukumomin kasar su samar da tallafi ga iyalan wadanda suka rasu, da mutanen da suka ji rauni.

Bayan abkuwar harin, wasu kungiyoyin kasa da kasa gami da wasu kasashe sun fito don yin Allah wadai da mummunan harin da aka kai kan wurin ibada, inda Sakataren Janar na MDD Antonio Guterres ya ce ya na taya iyalan wadanda suka rasu, da gwamantin da jama'ar kasar bakin ciki, ya na mai bukatar a gaggauta kamawa tare da gurfanar da maharan da suka tsere a gaban kuliya.

Ban da haka, babban sakataren kunigyar Musulmi ta OIC, Yousef bin Ahmad al-Othaimeen, ya furta a jiyan cewa, kungiyarsa tana goyon bayan kasar Masar kan matakan da take dauka domin don dakile ta'addanci, tare da jinjinawa jami'an tsaron kasar Masar kan yadda suke hattara da mayar da martani ga harin ta'addanci cikin sauri.

Shi kuwa Sakataren Janar na kawancen kasashen Larabawa (AL), Ahmed Aboul-Gheit, Allah wadai ya yi da harin, ya na mai kira ga kasashen Larabawa da gamayyar kasa da kasa su hada gwiwa wajen yaki da ta'addanci.

Haka zalika, ofishin jakadancin Amurka dake Masar, ya yi tofin Allah tsine kan harin da aka kai wa majami'ar, yana mai cewa Amurka na tare da jama'ar kasar Masar.

Ban da haka kuma, Jakadan Faransa a Masar Stephane Roumtier, ya bayyana a shafin sada zumunta na Twitter cewa, kasar Faransa za ta yi kokari tare da kasar Masar wajen dakile ta'addanci.

A jiya Juma'a ne, wasu maharan da ba a san ko su wane ne ba, suka farwa majami'ar Mar Mina dake cikin yankin Helwan na kudancin birnin Alkahira, fadar mulkin kasar Masar, inda a kalla mutane 10 suka mutu, yayin da wasu da yawa suka jikkata.

Haka kuma, jami'an tsaro masu aikin kwance bomabomai sun gano tare da kwance nakiyoyi 2 da aka dasa dab da majami'ar.

Wasu kafofoin watsa labaru na kasar Masar, sun ce kungiyar IS mai da'awar kafa daular Islama, ta sanar da daukar alhakin harin.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China