Jami'an 'yan sandan 3 suna aiki ne a filin jirgin saman kasa da kasa na Cairo, da wasu mutane biyar, ana zarginsu ne da laifin karba da kuma bayar da cin hanci domin samun damar haurewa da kudaden zuwa kasashen waje ta hanyar amfani da jami'an kwastam dake aikin bincike a filin jirgin saman kasar ta Masar.
A 'yan shekarun da suka gabata, kasar Masar ta sha kaddamar da shirye shirye na yaki da rashawa, wanda ya yi sanadiyyar kamawa da kuma garkame jami'an gwamnatin kasar masu yawa da wasu manyan ma'aikatan gwamnatin kasar, lamarin da ya baiwa kasar damar kwato makudan kudade. (Ahmad Fagam)