A ranar Talata ne, aka kaddamar da harin bom a filin jirgin saman Arish inda ya hallaka wani jami'i guda tare da jikkatar wasu mutane biyu, harin ya dan lalata jikin wani jirgin helikwaftan a lokacin ziyarar da ministan tsaron kasar Sedqi Sobhi dana cikin gidan Masar Magdy Abdel-Ghaffar suka kai filin jirgin saman, wadanda suka koma birnin Alkahira da yammaci
Kakakin shugaban kasar Bassam Rady, ya bayyana cewa, a lokacin ganawa tasu, shugaban kasar ya karbi rahoto daga wajen ministocin biyu game da yanayin tsaro da ake ciki a arewacin Sinai, da irin matakan da aka dauka domin yaki da ta'addanci, kana da irin matakan da aka dauka don tabbatar da tsaro da zaman lumana a yankin.
Taron ganawar ya hada da shugaban ma'aikatan kasar da babban jami'in tattara bayanan sirri na kasar da kuma shugabannin hukumomin tattara bayanan sirri na sojojin kasar.(Ahmad Fagam)